NASIHA
DAGA HUKUMAR A DAIDAITA SAHU, KANO STATE
(BANGAREN
RASHIN DA'AR MA'AIKATA)
Na
SADISU
MUSA MANDAWARI
1
"Aminu da Usman abokan juna ne,
tare suka tashi, tare sukai karatu, Aminu Turanci ya kaanta a jami'ar Bayero ta
Kano, shi ko Usman ya karanta lissafi ne a jami'ar Oxford ta
Ingila, tare suka fara amma Usman ya riga Aminu gamawa saboda wahalar karatu a
Najeriya, sannan wasu matsaloli sukan tasowa jami'o'in Najeriya a kullesu.
A yanzu dai sun gama karatu, kuma sun
sami sakamako irin wanda duk wani dalibi ya ke so ya samu malamai da abokan
Usman suna matukar kaunarsa, saboda da'arsa, da kuma hakurinsa.
Abokan Aminu da Usman, sun haxu sun
shirya musu walimar gama karatu lafiya da samun sakamako mai kyau.
Karamci da zumunci da 'yan uwanta da
Aminu da Usman su ka gani ja wurin abokansu shi ne ya sasu zubar da hawaye,
wanda a lokacin da aka nemi su yi jawabin godiya, hakan ta qi samuwa saboda a
lokacin ne hawaye ke zuba daga idanunsu, na farin ciki.
Malam Bako kwararre ne a harkar koyarwa
shi ne aka roka ya yi jawabi a matsayinsu, a karshe aka yi addu'a aka baje.
Bayan sati daya, Aminu ya zo wurin
abokinsa Usman, don su yi shawara su ga wanne aiki ya dace su nema, bayan sun
gama gaisawa shi kuma Aminu ya huta sai ya ce "Usman na zo ne mu yi
shawara, mu ga wanne aiki ya dace mu nema?" Sai Usman ya ce "Aminu ni
fa na tsorata da aiki a karqashin gwamnati, sai Aminu ya ce haba Usman in ba mu
yi wa gwamnatin jahar mu aiki ba to ai mun ci amanar ta, domin da kudin wannan
jiha tamu mu kai karatu tun daga firamare har zuwa jami'a gaskiya ne Aminu,
Usman ya fada to wai me ya tsorata ka ne Usman da ba ka so ka yi aiki a
gwamnatin jihar ka?" Aminu ya tambaye shi cikin mamaki.
Usman ya yi shiru na dan wani lokaci,sannan
ya daga kai ya kalli Aminu ya ce "Aminu rashin da'a da rashin ganin girman
na gaba, a cikin gwamnati uwa uba bayyana sirrin gwamnati da ya yi katutu a
zukatan ma'aikata a yau, ina so ka sani, Aminu babu wata ma'aiakta da take karkashin
gwamnati a yau da ma'aikatanta suke da cikakkiyar da'a da boye sirrin wannan
ma'aikata. Cikin nutsuwa, da sanyin murya, Usman ya ce "Aminu yau ta kai
hatta gidan gwamnati ba shi da sirri saboda rashin xa'ar ma'aikata, Aminu ya ce
ni abin da nake so Usman shi ne ba ka bani misalan irin rashin da'ar ma'aikatan
sunann ka bayyana mini wanne irin sirri ne suke bayyanawa? Ta haka zan gamsu
cewa gaskiya ka ke faxa mini don kaima
kada ka rufta cikin 'yan jita-jita, kuma ina so ka sani Usman kai fa ka na da
na'urar dake yi ma saiti, to ka gama?" Usman ya tambayi Aminu, na zo mdai
aya Aminu ya faxa, to ina so ka saurara ka ji irin rashin xa'ar ma'aikatan
wannan jiha tamu mai albarka, da kuma irin yadda suke bi suka bayyana sirrin
gwamnati ka ga dai da farko ma'aiakatan gwamnati irin su:-
1. Ma'aikatar ilimi
2. Ma'aikatar tsara birane
3. Ma'aikatar gona
4. Ma'aikatar lafiya
5. Ma'aikatar ayyuka da gidaje
6. Ma'aikatar watsa labarai
7. Ma'aikatar qananan hukumomi
8. Ma'aikatar harkokin mata
9. Ma'aikatar ruwa
Wadannan kasan ne daga cikin ma'aikatan
da suke qarqashin gwamnatin jiha amma rashin da'a da bayyana sirrin waxannan
ma'aikata ya yi katutu a zukatan ma'aikatan, bari in dau uku daga ciki in kawo
irin rashin xa'arsu da bayyana sirruns wanda bai dace su yi haka ba.
MA'AIKATAR ILIMI
Yau in kwamishina ya yi mitin da
sakataren sa, ko daraktocin sa, kafin shugabannin makarantu su ji, mutanen gari
sun ji kana shugaban makaranta amma sai ka ji wani zauna gari banza yana baka
labarin abin da zai faru a makarantar ka gobe.
Wani lokaci kuma malamai sune suke
zuwar wa da shugabannin makarantar abubuwan da ma'aikatar ilimi take tsarawa
makarantu.
Kai wani lokaci malami za a tura wata
makaranta amma sai shugaban makarantar bai sani ba, haka kuma za a daukeshi bai
sani ba.
MA'AIKATAR KANANAN HUKUMOMI
Sau da yawa za a tsara wani abu da za a
yi a wata qaramar hukuma a wani kauye, amma kafin bayanin ya je wurin shugaban
wannan karamar hukuma daga jaha tuni labarin ya je wurin mutanen wannan karamar
hukuma sai daga baya bayani a rubuce ya isa karamar hukuma.
MA'AIKATAR GIDAN GWAMNATI
Yau duk wani abu da gwamna zai tsara in
dai ya fito da shi daga zuciyarsa wasu su ka ji cikin wata daya zuwa biyar wasu
sun watsa labarin cikin gari, wadanda ya dace su ji a tsarin gwamnati sai dai
daga baya su ji ko takarda ta iso wurinsu bayan abu ya zama tsohon ya yi.
Usman ya ci gaba da cewa Aminu sirrin
gwamnati yana fita ne ta hanyar matan ma'aikata, ko kuma ta hanyar sakatarorin
gwamnati ko kuma ta hanyar yaran ma'aikata ga misali;
In aka yi mitin da wani darakta da ya
zo gida in hira ta yi dadi da matarsa sai ya hau zubar mitin din da aka yi da
shi, ita kuma da ta kwashe sai ta bayyanawa wata kawar ta shirye-shiryen
gwamnati.
Wani lokaci kuma sakatarori ne da an
aiko da wani bayani daga gidan gwamnati zuwa ma'aikatarsu da ya gani sai kwafi
na takardar ya saye ya fita da ita don kawai a ce ya burge su ne gwamnati.
Wani lokaci zumudin wani shugaba ne da
an yi mitin da shi in ya dawo gdia sai ya kirawo wanda akai mitin din a kan su,
ya ce.
"Kai wannan maganar mun gama da
ita jiya kuma kana ciki, in kuma wani abu ne sai ya ce dashi ka je ba wani abu
da ya faru, to daga nan fa shi wnanan zai shiga kwaza maganar, kusan wadannan
su ne hanyoyi da sirrin gwamanti ya ke fita.
Amma batun rashin da'ar ma'aikata a
wannan fili yake ba sai na tsaya yi maka wani dogon bayani ba.
Yau lebura zai iya sharrin da ya ga
dama ga shugabansa, shi kuma shugaba zai iya zubarwa da kansa mutunci a gaban
ma'aiaktansa bai damu ba saboda yana ganin shi ne shugaba,
Bayan duk Usman ya gama dogon bayaninsa
sai Aminu ya ce to Usman ni kuma sai ka saurareni don ka ji nawa batun.
"Ka sani Usman bamu da wata jaha
da tafi wannan jaha tamu idan har muka tsame hannunmu to waye zai zo ya gyara
mana?" Bayan mu ne 'yan gidan kuma mune muka san maganin wannan cuta
saboda da haka shiga za mu yi har Allah ya kai mu ga teburin da ya ke da qarfin
ikon hana wasu mugayen ayyuka ga ma'aikatan gwamnati.
Ina so ka sani Malam Usman wanke
zuciyar mu za mu yi, mu tsaya tsayin daka mu ga mun daidaita sahun ma'aikatan
wannan jaa ta mu.
Bayan Aminu ya wayar da kan Usman
abokinsa, sai ya yarda ya amince zai nemi aiki a gwamnatin jahar sa.
Bayan kwana biyu suka rubuta wasikun
neman aiki inda cikin wata daya aka dauke su.
Kowa ya sami aiki a inda ya dace dashi
saboda shi Aminu da ya karanta Turanci an kai shi KERD bangaren kula da da
jarabawar Turanci a matsayin sakataren darakta, shi kuma Usman bangaren akawun
na jiha a matsayin mai binciken kudi na jaha.
Cikin kanqanin lokaci 'yan bani na iya,
'yan tumasanci, 'yan hana ruwa gudu su kai ca zuwa ofishin su.
Da mutane suka ga sun zo da kwakkwarar
niyya sai surutai sai sharri suka fara tasowa, wasu suna cewa sa yi sa gama,
wasu suna cewa anyi wadanda suka fi su amma yau suna ina duk wadannan batutuwa
da suke faruwa suna ji amma sai suka yi shiru don su cimma burinsu.
2
Bayan shekara goma sha biyu da fara
aikinsu a ma'aikatun gwamnati sai da'ar su da kwazan su da dagewar su kan
gaskiya ta futo a fili sannan sai ya zama duk wani gwamna da ya zo sai ya tafi
da su.
"A kwana a tashi sai daya daga
cikin su ya kama rashin lafiya kamar ya mutu shi ne Usman saboda shine yafi
shiga matsala kasan cewar ya zama babban mai binciken kudi na jiha amma Allah
cikin rahamar sa ya bashi sauki kuma yawar ke sarai kamar baiyi ba.
Kimanin kwana uku kenan ana bayyana
cewa gwamna zai yi sauye sauye a gwamnatin sa gaba daya saboda yaga mafi yawan
ma'aikatun jihar masu aiki a wurin ba su da da'a sannan sirrin gwamnati yaki
buya musamman gidan gwamnatin kanta.
Kafin gwamna ya yi jawabi sai da ya
shawarci na kusa da shi a kan yana so a bashi sunayan mutane masu da'a da kwazon
aiki, a cikin mutum goma da gwamna ya nema su lalubo masa mutane masu kwazo
mutum shida sunan, Aminu su ka bayar mutum uku kuma suka ba da sunan Usman
mutum daya kuma shi ne ya ba da sunan wani dan jarida.
"Yau ita ce rana da mafi yawan
ma'aikata su ka kasance a gidajansu saboda suna saurarar lokacin da gwamna zayi jawabi da misalin 5:30 zuwa 6:00 P.M.
" lokaci na cika gwamna ya fara da
sunan Allah da yabo da Annabi Muhammad (S.A.W) sannan ya yabawa kwazon wasu
ma'aikatu ya kuma zargi wasu a karshe ya bar wasu ba yabo ba suka.
"Kai tsaye gwamna ya ya bawa
mutanen gari, da wasu mutane masu san kawo zaman lafiya a jiha sannan ya ciga
ba da cewa na san yau kusan wata shida al'ummar wannan jiha tamu mai albarka su
ke sauraran suji jawabina amma shiru sai yau Allah ya nufa.
"Bayan gwamna ya gama jawabin sa sai
ya ba da sanarwar cire kwamishinoni har guda (5) tare da sakataran sa, sai gari
ya dau sowa wasu suna godewa gwamna saboda suna ganin yan zu gyara zai zo, amma
wasu tsiraren mutane yan hana ruwa gudu suna ganin gwamna ya yi bambarama, ya
kashe kansa domin wadanda ya cire su ne shi ba zai iya komai ba sai da su.
Gwamna yaci gaba da cewa ya nada Aminu
a matsayi sakataren gwamnati sannan ya yi sallama aka saka taken qasa.
Bayan wata daya da rantsar da sababbin
kwamishinoni da sakataren gwamnati sai aiki ya kankama kowa ya shiga taitayin sa.
Tsari farko da Aminu ya fara aiwatarwa
shi ne mitin da daraktoci ya bayyana musu cewa za a basu miliyan 20 a kowacce
ma'aikatar su dan su yi gyare-gyare.
Cikin kwana daya sai ya ji magana ta
watsu a ma'aikatu da cikin al'umma, cikin gaggawa ya tara wadanda ya yi mitin
da su ya tambayesu yaya haka ta faru? Shiru ba amsa, amma a satin aka sauya
musu ma'aikata sannan aka hada musu da takardar jan kunne.
Haka sakataren gwamnati Aminu ya ringa
aiwatar wa daya bayan daya ba tsoro ba ja da baya bisa yardar gwamna sai gashi
sama da rabin ma'aikatu sun gyara.
Akwai wata matsala da taki ci ta ki
cinye wa a ma'aikatun gwamnati ita ce ta boye fayel din ma'aikata amma cikin
sauki aka sami warwarewar al'amura cikin sauki.
Bayan komai ya sami daidaita a harkokin
gwamnati sai gwamna ya tara kwamishinoninsa ya bayyana musu cewa, ya zama
wajibi kowa ya ji tsoron Allah ya sani duk wata nasara da su ke samu ta na
samuwa ne sakamakon tsarkake zuciya da ma'aikata suke yi ahalin yanzu.
Daga nan sai mai girma gwamna ya ce
yanzu kasancewar da'a da sirrin gwamnati sun sami gindin zama a halin yanzu to
ya zama wajibi a baiwa ma'aikata duk wani hakkinsu.
Cikin shekara daya da watanni ya zama
wannan jiha ta zama abar koyi ga sauran jihohin kasar.
Karfe 8 na safe kowanne ma'akaci na
wannan jiha ya isa wurin aikinsa saboda shima yana samun abin da ya dace a
msatainsu na ma'aikaci.
Alhamdulillahi
Sadisu Musa Mandawari.
Comments
Post a Comment